Monday, 8 September 2025

Rashin samun sukuni.Raunin kwakwalwa.Yawan kunci a kirji.Zubewar gashi.Rashin son zaman lafiya da matar ka, da mutanan gari.Rashin son shiga jamaa.Rashin son zuwa makaranta.Rashin son zuwa wajen Sana'a ko aiki.Zafin ciki,da zafin baya.Yawan zubar ciki wanda yamaimaitu.Karkacewar wata gaba.

Domin war ware sihir.
Yawan samun damuwa koda yaushe.
Rashin samun sukuni.
Raunin kwakwalwa.
Yawan kunci a kirji.
Zubewar gashi.
Rashin son zaman lafiya da matar ka, da mutanan gari.
Rashin son shiga jamaa.
Rashin son zuwa makaranta.
Rashin son zuwa wajen Sana'a ko aiki.
Zafin ciki,da zafin baya.
Yawan zubar ciki wanda yamaimaitu.
Karkacewar wata gaba.

Zaa iya neman waraka ta hanyar wanka da zaitun, ko shafawa tare da wasu itatuwan muslunci

"Manzon Allah Saw.Yan cewa: Kuci zaitun, kuma kushafa shi ajikin Ku, domin shi zaitun yana zuwa ne daga itaciya mai albarka"
Mafificiyar hanya wanda aka jarraba amfani da shafa man zaitun da kuma yin wanka dashi itace kamar yadda bayani zai to:

(1)Musamman samun man zaitun sai akaranta masa ayoyin Allah sai arika shafawa.

(2)Yin wanka da shafa man zaitun wanda aka hada da wasu itatuwan muslunci.

Domin haka wasu masana sukayi iya bakin kokari wajen hada man zaitun, da wasu itatuwan muslunci, da kuma huranni, domin wannan man zaitun din yakara wasu faidodi da kuma amfani, domin warkar da wasu cutuka, da kuma azabtar da shaidanun #Aljannu

Wasu daga cikin wadannan itatuwan muslunci din sune:

1—Zaa samo (1)liter na man zaitun
2—Habbatusauda cokali uku
3—Ganyan sazabu cokali uku
4—Kisdul Hindi cokali uku

Sai ahada waje daya adora akan wuta Mara karfi, sai azuba Jan miski,ko bakin miski ko ahada duka sai akaranta ayoyin ruqya aciki.

Sai arika shafawa da daddare lokacin kwanciya, da safe kuma sai ayi wanka.

Masu fama da ciwan Kai, zubar gashi, yawan damuwa koda yaushe, raunin kwakwalwa, sai surika shafawa akai.

Masu fama da matsalar yawan bugawar zuciya, ko faduwar gaba, ko yawan wasu wasi, ko yawan jin tsoro, surika jin basu kaunar matansu, ko bata kaunar mijinta yawan husuma ga ma aurata, rashin son zaman lafiya, agida da kuma mutanan unguwa.

Rashin son neman nakai, rashin son zuwa kasuwa, wajen aiki, rashin son shiga jamaa,rashin son yin ibada, rashin son zuwa makaranta da kuma karatu.
Sai surika shafawa a fuska, da kuma kirji, ko dukkan jiki baki daya.

Mutanan dake fama da matsalar zafin ciki,zafin baya, matsalar haihuwa wanda ake samun yawan bari.
Sai surika shafawa aciki, da kuma baya.

Amma wasu maluman na ruqya suna ganin shafawa a dukkan sassan jiki acikin wadannan matsalolin daaka ambata baki daya yafi bayar da faida sosai.

Kuma shafa wa sau daya a yanayin mai sauki, shafawa sau biyu a yanayin wanda ya tsananta.

Ga wata shawara wanda yake fama da zafin jiki kada yashafa man zaitun har sai yayi wanka ya sanyaya jikinsa sannan yashafa.

Ansamo wadannan bayanai ne daga cikin littafin (Lakdull mirjaal)
Jazakumullahu bikhair allahumma ameen.

Aljerian Islamic Chemist

No comments: