Gabatarwa: Jikin 'dan adam na bukatar wani irin
nau'in sinadarin suga (glucose) dake cikin jini
domin aiwatar da wasu daga cikin manya-manyan
ayyukan da suka shafi lafiyar jikin. Suga (glucose)
na bayarda kuzari (energy) ga jikin 'dan adam
wanda ake bukata wajen narkarda abinci da kuma
rayuwar 'kananan halittun da suka tattaru yawa
sukayi ginin jikin 'dan adam ko halittarsa tamkar
bululluka [tubali] (cells). Wannan sugan 'glucose'
shine makamashin dake bawa jikin 'dan adam
kuzari domin rayuwa. Kuma ana samun sa ne
daga abincin da muke ci - wato nau'in abinci mai
samarda kuzari (carbohydrate), kamar irinsu gero,
dawa, masara ,shinkafa da sauransu. Kwalwa
(brain), wayoyi ko hanyoyin sadarwar kwalwa a jiki
(nerves) da kuma wasu jajayen halittun jini
( developing red blood cells) , duk kaninsu suna
amfani da wannan makamashi (glucose) domin
samun rayuwa.
Ciwon-suga (diabetes) cutace wadda suga
(glucose) dake cikin jini yake haurawa sama -
wato suga yayi yawa a cikin jini. Yawansa nada
illa ga lafiya. Dalilin yawansa na faruwa ne sabili
da jikin mutum baya samarda da wani sinadarin
kemical mai suna 'insulin' ( = type 1 diabetes) , ko
jikin ne baya amfani da 'insulin' yadda ake so, ko
kuma ma jikin baya samar da 'insulin' da kyau
[wato isasshe] ( = type 2 diabetes). Idan har babu
'insulin' tofa sugan 'glucose' zai cigaba da taruwa
da yawa cikin jini har yayi illa ga lafiya. Sinadarin
'insulin' (a hormone), saifar 'dan adam ce ke
samar dashi (pancreas). Amfanin sinadarin
'insulin' shine daukar sugan 'glucose' dake cikin
jinin zuwa cikin 'kananan halittun da sukayi ginin
jikin 'dan adam (cells) domin samun kuzari gare
su da cigaban rayuwa. Idan babu 'insulin' ko baya
aiki yanda ake bukata to suga fa zai cigaba da
taruwa cikin jini yayi yawa har ya haddasa
munanan matsaloli ga lafiya. Sugan zai iya yin illa
ga idanu, koda, wasu jijiyoyin jini da kuma
wayoyi/hanyoyin sadarwar kwalwa a jiki. Ciwon-
suga zai iya haddasa cutar zuciya, mutuwar
sashen jiki koma ya jaza yanke kafar marar-
lafiyar. Idan ciwon yayi 'karami zai iya haddasa
matsalar 'kashi da gabobi, matsalar fata, matsalar
narkewar abinci, rashin karfin mazakuta, matsalar
hakora da dasashi. 'Type 2 diabetes' ,wato nau'in
ciwon-suga na 2 da mukayi bayani (wanda jiki
baya amfani da 'insulin' yadda ya dace) shine
nau'in ciwon-suga da yafi yawa ga mutane da
dama fiye da nau'in ciwon-suga na 1: 'type 1
diabetes' (wanda mu kace jiki baya samarda da
sinadarin 'insulin').Alamomin Ciwon Alamomin
Ciwon-suga Nau'i na 1 (type 1 diabetes
symptoms):
• Yawan jin kishirwa sosai
• Yawan yin fitsari
• Yawan jin yunwa ko gajiya
• Raguwar nauyin mutum ba tare da mutum yayi
kokarin ragewar nauyin ba
• Dadewar ciwo/gwambo bai warke ba/warkewa a
hankali
• Rashin gani da kyauAwon jini zai iya nuna idan
akwai ciwon ko sabanin haka. Idan akwai irin
nau'in ciwon , toh mutum zai cigaba da amfani da
sinadarin 'insulin' da aka samar a asibiti, za'a
bashi sinadarin a asibiti akan 'ka'ida da umarnin
'kwararren likita. Anfi yawan samun 'kananan yara
da matasa da irin wannan nau'in ciwon-suga
(Juvenile diabetes/Insulin-dependent diabetes)duk
dadai cewa zai iya shafar mutane a kowani
shekarun su na rayuwa. Alamomin Ciwon-suga
Nau'i na 2 (type 2 diabetes symptoms):
• Yawan jin kishirwa sosai
• Yawan yin fitsari
• Yawan jin yunwa ko gajiya
• Raguwar nauyin mutum ba tare da mutum yayi
kokarin rage nauyin ba
• Bushewar fata, kaikayin fata
• Mutum yaji kamar ba kafarsa ba ko jin tsira a
kafafu
Yin awon jini a asibiti ko wata ingantacciyar
cibiyar lafiya zai iya nuna maka ko kana da ciwon
suga ko kuma akasin haka. Motsa-jiki (exercise),
rage nauyin jiki yanda ya dace dace da koyarwar
cikon lafiya, da kuma kula da tsarin cin abinci
daya dace da ciwon lafiya, ko shakka babu , zasu
taimaka sosai wajen shawo matsalolin lafiya na
ciwon-suga. Cututtukan saifa, magunguna,
kemikals, kamuwa da wasu cututtukan da gado
daga mahaifan mutum na daga cikin dalilin da
ake alakantawa da suke haddasa ciwon-suga.
Allah ya bamu lafiya. AMEEN.
Munada ingantattun magunguna kala daban daban akan ciwuka kamar, hawan jini, asama,tari,suga, shafar jinnu dadai sauransu,kala daban daban, kuma insha Allah ana samun waraka tahanyar amfani damagungunan mu. Kuma muna ingantattun magunguna kan shafar jinnu ko sihir,maita dadai sauransu zaasamemu masallacin Janihouse no.08152753609/08062264060.kota email:rahamaniyyaislamicmedicine@gmail.com
Monday, 24 October 2016
Ciwon sugar da illolinsa
Amfanin naa naa
Na'a-na'a [Peppermint/mentha piperita or mint]
wata shuka ce mai albarka da ake amfani da ita a
matsayin maganin gargajiya. Ganyen na'a-na'a
kore ne, kamshin ta nada karfi, tana da kamshi
mai dadin gaske da filebo mai sanyaya rai. Na'a-
na'a nada sinadarin 'minti' ( wato 'menthol') mai
sanyaya rai da lafiyar jikin dan adam. Akanyi
amfani da na'a na'a wajen sarrafa wasu kayan
amfanin gida da muke siya na yau da kullum,
wato kayan amfani da muke siya a kasuwa kamar
irinsu makilin (toothpaste), sabullai (soaps), man-
shafawa (creams and vaselines), cingam (chewing
gum), sinadarin wanke baki (mouthwash) ,
magungunan shafawa (ointments), da sauransu ,
saboda kamshinta da amfaninta ga jikin dan
adam.
Bincike ya nuna cewa, shukar na'a-na'a dai ta
samune asali ta hanyar auren-shuka , wato auren
shuka mai suna 'watermint' da turanci da kuma
wata shukar mai suna 'spearmint'. Bincike ya nuna
cewa na'a na'a tazo ne daga kasashen turawa da
larabawa. Mutanen wadannan kasashen da muka
ambata kanyi amfani da ganyen na'a-na'a cikin
abinci da kuma wajen shayi, a matsayin ganyen-
shayi (tea leaves) haka kuma, akwai man -na'a
na'a ( peppermint oil) da ruwanta (peppermint
water) a kasuwa domin amfani na daban-daban.
Bincike ya nuna cewa na'a-na'a nada amfani da
yawa ga lafiyar dan adam. Wasu daga cikin
amfaninta ga jikin mutum sune:
1. Tana magance matsalar bacin-ciki da rashin
fitar bahaya maisa tsugunni
a bayi.
(Ayi shayin na'a-na'a ko azuba manta cikin shayi
marar madara.)
2. Tana saukake narkewar abinci
3. Maganin tuka
4. Maganin gudawa
5. Maganin mura da tari [da kuma mura mai
damun makoshi - wato 'sore throat']
(ayi amfani da man na'a-na'a ko ganyen , a tafasa
ganyen ayi shayi marar madara
, haka kuma, za'a iya amfani da man na'a-na'a
cikin ruwan zafi, ayi turiri,
a lullube da mayafi).
6. Maganin ciwon-kai ( a shafa manta wajen da
kai ke ciwo).
7. Maganin ciwon-jiki ( a shafa manta ga jijiyoyin
jiki dake ciwo
ko wajen dake damunka da ciwo, zata sanyaya,
insha Allahu).
8. Maganin ciwon-hakori (ayi amfani da man na'a-
na'a da auduga,
a diga man ga auduga , sa'annan a lika ga hakori
mai ciwon).
9. Maganin kaikayi
10. Korar sauro ( a shafa man na'a-na'a ga jiki -
hannuwa da kafafu , sauro zai gujesu)
11. Kashe tsutsar ciki
12. Taimakawa hanta wajen aiki
13. Rage yawan damuwa
- tana sanyaya rai da hana damuwa
( a tafasa ganyen
na'a-na'a ayi shayi, ko manta a zuba cikin kofin
shayi , safe da yamma).
14. Tana taimakawa kwalwa wajen rike karatu da
kaifin fahimta (ayi shayi da ganyen na'a-na'a a
rinka sha da zuma).
15. Tana sanya girki yayi kamshi - filebo ( ayi
amfani da ganyen wajen girki).
Hakan zai taimaka wajen son cin abincin
(appetite), musamman ga wanda
baya son cin abinci.
16. Tana maganin ciwon-ciki , musamman ga
mata masu matsalolin al'ada.
17. Da sauransu.
Rahamaniyya Islamic medicine Funtua.
Amfanin kanin fari
1. Yana maganin ciwon hakori.
Zaka iya amfani da man-
kanimfari (clove oil) ga hakori
mai-ciwo ko kuma kanimfarin
(dakakke) , a jikashi kadan da
ruwa a lika wajen hakori mai-
ciwo. Idan mai ( clove oil) kake
amfani dashi sai asamu
auduga a zuba man kadan a
lika wajen hakori mai-ciwo (ka
danne da hakora).
2. Za’a iya amfani dashi a
matsayin abun wanke baki.
Yana maganin warin baki (a
tafashi a yawaita wanke baki
dashi sau 2 ko 3 a rana).
3. Yana hana zubar hanci ga
masu mura. A tafasashi da
citta/jinja (ginger) a sha shayi.
4. Yana maganin cututtuka
(infections caused by bacteria,
fungi and virus ) na cikin jiki ko
na bayan fata, kamar kuraje
(spots and rashes), makero
(ring worm) da kyanda
(measles).
5. Yana maganin zawo da
amai da zazzabin cizon sauro.
6. Yana saukake narkewar
abinci a ciki.
7. Yana maganin ciwon kai. A
shafa man kanimfari a
goshi.Yana taimakawa wajen
ciwon kai da mura kan jazawa.
8. Yana kara karfin mazakuta
idan aka shafa mansa kadan
ga mazakuta. Da sauransu
Saturday, 22 October 2016
Amfanin zuma
Taasirin jinnu akan zuciyar dan adam
Saturday, 15 October 2016
Saturday, 1 October 2016
علاج الضعف الجنسي بالأعشاب
خلطات للتقوية الجنسية عند الرجال خلطات للتقوية الجنسية عند الرجال احيانا يعاني الرجال لأسباب مختلفة من الضعف الجنسي وبدون أدوية يمكن علاج هذا الضعف كما يمكن تقوية القدرة الجنسية طبيعيا وهذا ما سوف نعرضه اليوم من خلال مجموعة وصفات وخلطات طبيعية ١٠٠٪ يمكنها حل مشاكل الضعف الذي قد يطرق بابك فجأة بدون سابق إنذار ما هو الضعف الجنسي لدى الرجال؟ الضعف الجنسي لدرى الرجال يحدث عندما لا يستطيع الرجل الحصول على الانتصاب الكافي للقيام بالعلاقة الحميمية، في بعض الأحيان لا يحدث ضعف الانتصاب إلا في أحوال معينة، أو قد يحدث لأسباب طبية مثل ضيق الأوعية الدموية، أو التغيرات الهرمونية، أو القلق أو الاكتئاب، أو مشاكل زوجية، أو إصابات. والأسباب السابقة يمكن التخلص منها بعلاجات منزلية طبيعية تزيد من قوة الانتصاب. علاجات طبيعية تساعد في تقوية القدرة الجنسية الجزر والعسل والبيض: علاج منزلي لضعف الانتصاب حيث يزيد من الرغبة الجنسية لدى الرجال. أضف 2 ملعقة كبيرة من العسل مع نصف بيضة مسلوقة، ونصف كوب من الجزر المبشور. اخلط المزيج جيداً قبل تناوله مرة في اليوم. تناول هذا المزيج لمدة شهر ونصف لتجد نتيجة مبهرة. خليط الزنجبيل والعسل: الزنجبيل معروف كمكون طبيعي لعلاج العديد من المشاكل الصحية، وكذلك هو مفيد للضعف الجنسي. قطع الزنجبيل لقطع صغيرة وحولها لمزيج متجانس. اخرج العصير من مزيج الزنجبيل. خذ 2 ملعقة صغيرة من مزيج الزنجبيل واضفها مع 2 ملعقة صغيرة من العسل. تناول الخليط ثلاث مرات في اليوم لمدة شهر. التمر المجفف والمكسرات: التمر يعطي قوة لجسم الإنسان، وكذلك يزيد من القدرة الجنسية لدى الرجال. اخلط مقدار قبضة يد من التمر المجفف مع المكسرات وحبوب الكينوا بكميات متساوية، واطحنهم وحولهم لبودرة ناعمة. امزج الخليط السابق مع كوب من الحليب وتناوله بصورة يومية. الزبيب: الزبيب مكون رائع لزيادة القدرة الجنسية لدى الرجال، ويمكن تناوله كالتالي. اغسل حوالي 30 جرام من الزبيب في ماء دافئ. اغلي الزبيب في 200 مل من الحليب، حتى تتنفخ حبات الزبيب. تناول الزبيب واشرب الحليب. تناول هذا المزيج ثلاث مرات في اليوم. البامية: البامية أحد أنواع الخضروات التي تزيد من الرغبة الجنسية لدى الرجال. اخلط 5 جرام من جذور البامية مع كوب من الماء الدافئ. اضف 2 معلقة صغيرة من الكسر إلى الحليب. تناول هذا المزيج يومياً حتى يختفي الضعف الجنسي. جذور الأسبرجس: جذور الاسبرجس مثيرة للرغبة الجنسية، وتساعد على التخلص من الضعف الجنسي وضعف الانتصاب. اضف 15 جرام من جذور الاسبرجس إلى كوب من الحليب. اغلي الحليب واتركه حتى يبرد قليلاً ثم تناوله. كرر هذا الوصفة حتى تحصل على النتائج المرجوة. الزعفران: الزعفران مكون معروف بقدراته على إثارة الرغبة الجنسية، وكذلك يساعد على التخلص من التوتر. ضع الزعفران في الطعام بصورة منتظمة. يمكن إضافة الزعفران إلى زيت طبيعي وإجراء تدليك للجسم بالكامل به. الثوم: الثوم إحدى الخضروات الطبيعية التي تثير الرغبة الجنسية لدى الرجال، وكذلك هو معقم طبيعي ويقوي الجهاز المناعي، ويزيد من قوة الانتصاب. امضغ ثلاث فصوص ثوم يومياً للحصول على نتائج سريعة. تناول الأطعمة التي تحتوي على الثوم بكثرة. البصل الأبيض: البصل معروف بقدراته على إثارة الرغبة الجنسية لدي الرجال. قطع البصل لشرائح ثم حوله لمزيج متجانس. ضع البصل مع ملعقة صغيرة من الزبدة على النار واضف عليهم ملعقة صغيرة من العسل. تناول هذا العلاج يومياً على معدة خاوية، ولا تأكل بعدها لمدة ساعتين. تناول هذا العلاج بصورة يومية يزيد من الرغبة الجنسية لدى الرجال. الراحة: حاول الاحتفاظ بعقلك بعيداً عن القلق خلال العلاقة الحميمية. لا تقلق كثيراً حول قدراتك اثناء العلاقة الحميمية. حاول اجراء تمارين لإرخاء العضلات والتحكم في التنفس. الإقلاع عن التدخين: حاول استخدام بدائل عن النيكوتين مثل اللبان أو السجائر الالكترونية بدلاً من التوقف عن التدخين بصورة مفاجئة. ستجد أن قدراتك الجنسية اختلفت بعد التوقف عن التدخين. تناول الأطعمة الغنية بفيتامين أ: تناول الأطعمة الغنية بفيتامين أ والتي تساعد على تحسين القدرة الجنسية.