Monday, 24 October 2016

Ciwon sugar da illolinsa

Gabatarwa: Jikin 'dan adam na bukatar wani irin
nau'in sinadarin suga (glucose) dake cikin jini
domin aiwatar da wasu daga cikin manya-manyan
ayyukan da suka shafi lafiyar jikin. Suga (glucose)
na bayarda kuzari (energy) ga jikin 'dan adam
wanda ake bukata wajen narkarda abinci da kuma
rayuwar 'kananan halittun da suka tattaru yawa
sukayi ginin jikin 'dan adam ko halittarsa tamkar
bululluka [tubali] (cells). Wannan sugan 'glucose'
shine makamashin dake bawa jikin 'dan adam
kuzari domin rayuwa. Kuma ana samun sa ne
daga abincin da muke ci - wato nau'in abinci mai
samarda kuzari (carbohydrate), kamar irinsu gero,
dawa, masara ,shinkafa da sauransu. Kwalwa
(brain), wayoyi ko hanyoyin sadarwar kwalwa a jiki
(nerves) da kuma wasu jajayen halittun jini
( developing red blood cells) , duk kaninsu suna
amfani da wannan makamashi (glucose) domin
samun rayuwa.
Ciwon-suga (diabetes) cutace wadda suga
(glucose) dake cikin jini yake haurawa sama -
wato suga yayi yawa a cikin jini. Yawansa nada
illa ga lafiya. Dalilin yawansa na faruwa ne sabili
da jikin mutum baya samarda da wani sinadarin
kemical mai suna 'insulin' ( = type 1 diabetes) , ko
jikin ne baya amfani da 'insulin' yadda ake so, ko
kuma ma jikin baya samar da 'insulin' da kyau
[wato isasshe] ( = type 2 diabetes). Idan har babu
'insulin' tofa sugan 'glucose' zai cigaba da taruwa
da yawa cikin jini har yayi illa ga lafiya. Sinadarin
'insulin' (a hormone), saifar 'dan adam ce ke
samar dashi (pancreas). Amfanin sinadarin
'insulin' shine daukar sugan 'glucose' dake cikin
jinin zuwa cikin 'kananan halittun da sukayi ginin
jikin 'dan adam (cells) domin samun kuzari gare
su da cigaban rayuwa. Idan babu 'insulin' ko baya
aiki yanda ake bukata to suga fa zai cigaba da
taruwa cikin jini yayi yawa har ya haddasa
munanan matsaloli ga lafiya. Sugan zai iya yin illa
ga idanu, koda, wasu jijiyoyin jini da kuma
wayoyi/hanyoyin sadarwar kwalwa a jiki. Ciwon-
suga zai iya haddasa cutar zuciya, mutuwar
sashen jiki koma ya jaza yanke kafar marar-
lafiyar. Idan ciwon yayi 'karami zai iya haddasa
matsalar 'kashi da gabobi, matsalar fata, matsalar
narkewar abinci, rashin karfin mazakuta, matsalar
hakora da dasashi. 'Type 2 diabetes' ,wato nau'in
ciwon-suga na 2 da mukayi bayani (wanda jiki
baya amfani da 'insulin' yadda ya dace) shine
nau'in ciwon-suga da yafi yawa ga mutane da
dama fiye da nau'in ciwon-suga na 1: 'type 1
diabetes' (wanda mu kace jiki baya samarda da
sinadarin 'insulin').Alamomin Ciwon Alamomin
Ciwon-suga Nau'i na 1 (type 1 diabetes
symptoms):
• Yawan jin kishirwa sosai
• Yawan yin fitsari
• Yawan jin yunwa ko gajiya
• Raguwar nauyin mutum ba tare da mutum yayi
kokarin ragewar nauyin ba
• Dadewar ciwo/gwambo bai warke ba/warkewa a
hankali
• Rashin gani da kyauAwon jini zai iya nuna idan
akwai ciwon ko sabanin haka. Idan akwai irin
nau'in ciwon , toh mutum zai cigaba da amfani da
sinadarin 'insulin' da aka samar a asibiti, za'a
bashi sinadarin a asibiti akan 'ka'ida da umarnin
'kwararren likita. Anfi yawan samun 'kananan yara
da matasa da irin wannan nau'in ciwon-suga
(Juvenile diabetes/Insulin-dependent diabetes)duk
dadai cewa zai iya shafar mutane a kowani
shekarun su na rayuwa. Alamomin Ciwon-suga
Nau'i na 2 (type 2 diabetes symptoms):
• Yawan jin kishirwa sosai
• Yawan yin fitsari
• Yawan jin yunwa ko gajiya
• Raguwar nauyin mutum ba tare da mutum yayi
kokarin rage nauyin ba
• Bushewar fata, kaikayin fata
• Mutum yaji kamar ba kafarsa ba ko jin tsira a
kafafu
Yin awon jini a asibiti ko wata ingantacciyar
cibiyar lafiya zai iya nuna maka ko kana da ciwon
suga ko kuma akasin haka. Motsa-jiki (exercise),
rage nauyin jiki yanda ya dace dace da koyarwar
cikon lafiya, da kuma kula da tsarin cin abinci
daya dace da ciwon lafiya, ko shakka babu , zasu
taimaka sosai wajen shawo matsalolin lafiya na
ciwon-suga. Cututtukan saifa, magunguna,
kemikals, kamuwa da wasu cututtukan da gado
daga mahaifan mutum na daga cikin dalilin da
ake alakantawa da suke haddasa ciwon-suga.
Allah ya bamu lafiya. AMEEN.

No comments: