Monday, 24 October 2016

Amfanin zaitun dangane da lafiyar dan adam, da kuma magani.

Amfanin Man-Zaitun ga Lafiya ( a
takaice)
Man-zaitun ( Olive oil/ Olea europea ) wani irin
nau'in mai ne da ake samarwa daga 'ya'yan
itaciyar zaitun (Olive tree). Ana amfani dashi
wajen girki, gyaran fata, magani, hada sabullai da
kuma man-fitila ( a gargajiyance). Man-zaitun ana
amfani dashi a 'kasashen duniya da dama,
musamman kasar Spain, France (Faransa), Italy,
Greece (kasar Girka), Syria, Lebanon, Egypt,
Libya,Tunisia, Algeria, Morocco da sauransu. Toh
amma kasashen da suka fi yawan amfani dashi
sune Portugal, Spain, Italy da Greece. Daga
shekara ta 2000 zuwa ta 2009, kasashe 3 da suka
fi yawan samar dashi sune: 1. Spain 2. Italy 3.
Greece. Kasar Syria itace ta 4 , sai mai-bimata
kasar Tunisia, a matsayin ta 5.
Sabili da muhimmancin itaciyar zaitun, Allah
Madaukakin sarki, Mai -halittu ya ambace ta a
cikin Al-Qur'ani Maigirma - Surat At- Tin da Surat
An- Nur.
Man-zaitun nada amfanin sosai ga lafiyar 'dan
adam. Binciken ilimin kimiyya ya nuna cewa yana
da amfani kamar haka:
1. Yana 'karfafa garkuwar jiki ( domin yaki da
kwayar cutar biras, bacteriya, fangas (fighting
virus, bacteria, fungus etc.) da sauransu.
Wadannan cututtuka suke haddasa matsalolin
lafiya da dama, kamar irinsu ciwon-anta, tetanus
da cin-ruwa.
2. Yana da sinadarai masu bada kariya daga
kamuwa da ciwon daji (rich in antioxidant
subtances).
3. Kariya daga cututtukan zuciya - yana rage
yawan sinadarin kolestirol (reducing high
cholesterol) wanda idan yayi yawa a cikin jini yake
da illa ga zuciya.
4. Rage hawan jini (reducing high blood
pressure).
5. Taimako ga masu ciwon-suga (helping diabetic
patients).
6. Kariya daga ciwon jiki (sanyin jiki) dana gabobi
(anti-rheumatism & arthritis).
7. Inganta lafiyar zuciya (improving heart's
function esp. to older people whose hearts are
weak due to aging) musamman ga tsofaffi wanda
zuciyar su ta fara rauni wajen aiki saboda tsufa.
Yana gyara zuciya da quruciya.
8. Kariya daga ciwon daji dake shagar fata
( protection from skin cancer).
9. Inganta lafiyar qashi. (improving bone health).
10. Inganta lafiyar kwalwa wajen koyon wani abu
kamar karatu ko rike karatun, musamman ga
manya (improving cognitive function) da
sauransu.
Ana iya amfani da man-zaitun kamar haka:
~ Asha cikin babban cokali sau 2 a rana - safe da
rana, cokali daya a kowane lokacin.
~ Ayi girki dashi a matsayin man girki ko a zuba
cikin abinci bayan girki.
~ Manshafawa kamar sauran man amfani na jiki.
~ Giris ga ma'aurata (sex lubricant). Bugu da kari,
zai kuma bada kariya daga cututtuka.
~ Ciwon-kunne, digo 2 ko 3 na man a cikin
kunne.
~ Da sauran wasu hanyoyin na inganta lafiya.
Allah Yasa mudace Ameen.

No comments: