Saturday, 22 October 2016

Taasirin jinnu akan zuciyar dan adam

Ansamo wani Hadisi daga dan Abbas (RA) yace:hakika Shaidanu sukan kashe zuciyar dan adam kuma sumakantar daita sumaidata tazama kamar yadda gawa take sai yadda akayi daita, to haka Shaidanu suke mayar da zuciyar wasu mutanan. Allah yahore masu shiga jikin dan adam ko ina shi yasa sai suka zabi zuciyar dan adam, domin daganan sakonni ke zuwa,akan cewa na aaikata kaza,aa koko dai nabar kaza,sai yazama zuciyar dan adam itace jagora agaba wajan kai ma dan adam hari,gabban dan adam kuma sai sumaida su Sune runduna,domin kusan Sune gaba wajan aikata sabo,Idan Shaidanu suka sami wannan dama akan dan adam, sai yazama gabbansa sun raunana, baya iya yin mallakar kansa wajan aikata sharri kowanne iri ne. Dan hakane Manzon Allah s.a.w.yace :Ajikin dan adam akwai wata tsoka Idan wannan tsokar ta gyaru to dukkan jikin mutum ya inganta, yakuma kubuta, yace kuma Idan wannan tsokar tabaci to komaima yabaci ajikin dan adam.... Yace wannan tsoka itace zuciya!!! Sai dai Hakika akwai wasu daga cikin mutane wadanda Allah (swt) yakewayesu da karfin imani, kuma yayi masu katanga daga tsoron sa, kuma masu gadin wannan katanga Sune zikrora dayake yi babu tayadda zaayi irin Wadannan Shaidanu susami nasara akan wannan dan adam din. Shi yasa Manzon Allah s.a.w.yace ga sayyina UMMAR Dan kadab (RA) yace ina rantsuwa dawanda rayuwata take a hannun sa, yace ya UMMAR babu yadda zaayi shaidan yayarda yahadau dakai akan hanya, face daya hangoka dole sai yasake wata hanyar wanda ba wannan ba wanda kabiyo. Wikayatul insane, ta Warhead Abdulsalam Bali.Shafi na 135. Yakai dan uwa, yar uwa ka/kizama mai tsoron Allah aboye, ko a bayyana, ka/kizama mai yawan azkar, dakuma kiyaye dokokin Allah, sai Allah yabaki/ka kariya irin wanda yabawa sayyadina UMMAR (RA) yahana Shaidanu zuwa inda kake kwata kwata. Allah kakare mu daga dukkan sharrin shaidanun mutane da kuma aljannu Ameen. Rahamaniyya Islamic medicine Funtua.

No comments: