Saturday, 3 February 2018

Maganin Fitsarin kwance

Assalamu alaikum malam yaro ne yake fitsarin kwance yakai shekara shabiyar ahalin yanzu bai dainaba amma bakullun yakeyiba kuma sautarima sai da sanyi cutane ? Ko kuma da bi ar wasu yaran ne haka zaidai na? afahimtar dani Dr dan Allah?

Waalaikumu Salam
Abinda su masana suke cewa akan irin wannan matsalar shine
Sukan kasa matsalar kamar gida uku
Nafarko akwai yanayi wanda yake sananne kamar yadda dama ansan wannan yaro idan yana karami yakanyi fitsarin kwance amma zuwa wani lokaci idan yafara girma sai yabari.
Nabiyu kuma akwai yaron dayake dadewa bayan yafara girma amma dai kaga yajima bai daina fitsariba akwance.
Na uku shine wanda ya girma ko ya kai matsayin da ya balaga koma yazama babban mutum amma yana fama da wannan matsala mace ko namiji, to likitocin muslunci abinda sukace aduba shine :Yakanyi mafalki yagan shi abayi sannan yafalka kawai sai yaga yayi fitsari a kwance. Kokuma baa samun hakan kawai sai dai yaga yayi fitsari a kwance. To malaman muslunchi abinda ake kaddara wanann shine wata kila baya rasa nasaba da matsalar sharrin shaidanun aljannu, ko sihir, domin yin mafalkin fitsari, ko mutum yayi mafalki yagan shi abayi yana fitsari kuma yafalka yagan shi yayi fitsari a kwance to wannan ma baya rasa nasaba da matsalar jinnu. Kamar yan mata masu fama da irin wannan larura zaka samu shaidanun aljannu suka sabbabar masu, koko wasu samarin wadanda tsoron ALLAH yayi karanci a zukatansu sukan sa ayima budurwa sihir domin bata sonsu,kokuma susa ayi mata sihir tare da tura mata shaidanun aljannu domin hanata sakewa...... Dukan wannan babu wanda bamu ganiba..... Allah shi karemu Ameen.
Hanyar neman waraka ga yaron da ya girma yana fitsarin kwance ko babba wanda ya girma amma yana fitsarin kwance to kodai wanne irin matsalar yajawo hakan..... Matukar dai bawai wata sananniyar larura bace wanda dama ansan takan haifar da hakan to abinda zaayi shine, Zaasamo garin habbatisauda, garin hulba, garin kusdul hind,da tsamiya zaa hada garukan waje daya sai arika tafasawa cokali daya, tsamiya kwara daya, bayan ansauke antace sai ayi masa rukyah wannan hadin maganin ko akaranta, fatiha, ayatul kursiyu, amanarasul, kulya kulhuwa, falaki da kuma nasi. Acikin sai lokacin da zaa kwanta sai ayi bisimillah asha.

Haka zaaci gaba dayi Insha Allah har asami waraka.
Amma idan antabbatar cewa akwai sharrin shaidanun aljannu aciki, ko sihir, to zaa iya hadawa da maganin da muka kawo rannan wato # ZUYUTUL_ASHARA sai adinga shafa wa idan zaa kwanta, kokuma akwai wani maganin mu mai suna # Naru_shayadin -wutar aljannu shima yana taimakawa matuka wajan magance matsalar shaidanun aljannu, ko sihir insha ALLAH, zaa iya amfani dashi.
Dafatan ALLAH yasawake Allah yasa adace Ameen.

No comments: