Sunday, 8 October 2017

MAGANIN KOWACCE IRIN CUTA DA IZININ ALLAH

MAGANIN KOWACCE IRIN CUTA DA IZININ ALLAH
'Yar uwa ta Musulma, Dukkan abinda ya samu bawa, to
jarrabawa ce daga Ubangijinsa. kuma akwai falala mai girma
wacce bayin Allah suke samu idan sunyi hakuri bisa duk irin
jarrabawar da ta samesu.
Kiyi hakuri ki dage da addu'a irin ta Annabi Ayyub (as) "RABBI
INNEE MASSANIYADH DHURRU WA ANTA ARHAMUR
RAHIMEEN". duk lokacin da kikayi sujjada acikin sallarki.
Sannan ki samu Man Zaitun mai kyau (Extra Virgin Olive oil)
tare man Habbatus Sauda 'Dan Misra ko kuma na kampanin
Hemani. ki hadasu waje guda ki tofa wadannan addu'o'in
acikinsa sannan ki rika shafawa kuma kina sha:
1. FATIHA 7
2. AYATUL KURSIYYI 33
3. LA ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNEE KUNTU MINAZ
ZALIMEEN 11.
4. INNE MASSANIYADH DHURRU WA ANTA ARHAMUR
RAHIMEEN 41.
5. QUL HUWALLAHU 33.
6. SURATUL FALAQ DA SURATUN NAAS 33.
7. ALLAHUMMA RABBAN NAAS AZHIBIL BA'AS WASHFI
ANTASH SHAAFEE, LA SHIFA'A ILLA SHIFA'UKA. SHIFA'AN
LAA YUGHADHIRU SAQMAN (kafa 3).
8. AS'ALUL LAHAL AZEEM RABBAL ARSHIL AZEEM AN
YASHFIYANEE (kafa 7).
9. Salatun Nabiyyi (saww) kafa 10.
10. Ayatush shifa'i kafa 7.
Ki tofa aciki sannan ki rabashi gida biyu, ki rika shan rabi. rabi
kuma kina shafawa ajikinki. Shi wanda zaki sha din, zaki iya
hadawa da zuma kina sha.
Kuma zaki iya tofawa acikin ruwan zamzam ko ordinary water
ki mayar dashi shine ruwan shanki ko yaushe.
INSHA ALLAHU ko ma wacce irin chuta ce ajikin mutum yake
fama da ita, in dai yayi amfani da wannan addu'o'in da aka
tofa, to zai samu lafiya da izinin Allah. mutukar dai yayi imani
da Allah da Manzonsa, kuma ya yarda cewa Alqur'ani yana
magani..

Allah yabamu dacewa Allahumma amen

No comments: