Wednesday, 2 November 2016

HANYOYIN DA ZAA IYA SAMUN WARAKA DAGA MATSALAR NA ININA, DA KUMA MATSALAR NAUYIN HARSHE.

Daga bincike na manyan likitocin muslunci dangane da shawarwarin da suka bada wajan magance matsalar inina, dakuma nauyin harshe.

Kamar yadda Jamaa dadama sunsha yi mana wadannan tambayoyin.

(1)Zaasamo wani magani daake cemasa falfal aswad, da kuma kisdu,yawansu yazama daya, sai ahada da zuma, da zait (kirdal) sai adinga sha sau uku cokali uku arana  insha Allah zakadace.

(2)Zaa samo habbatirashad rabin kofi, habbatirashad rabin kofi, kishiru rabin ruman rabin kofi, (Mur) cokali daya, sai ahada da zuma lita 2 zaadinga sau uku arana cokali daya daya insha Allah zaa dace.

(3)Kokuma abi wannan hanyar :
Asamo zabib, dakuma danyan citta atafsa zaa rika shan wannan hadin maganin tun da asuba kafin akarya.

(4)Ko abi hanyar na hudu :Zaasamo ganyan (#kabeji) sai adinga cinsa da daddare kafin akwanta barci.

Sai kuma abubuwan da zaa iya sha su kuma akan wannan matsalar kamar haka :
(1)Zaarika shan (Lubanazakar) wanda aka tafasa.

(2)Ko asamo (Sukarin Nabat) arika tafasa wa anasha sau biyu arana.

(3)Ko asamo yayan habbatibaraka adebo karamin cokali atauna azuba ruwa ashanye. Dakuma gab da zaa kwanta Insha Allah zaa samu biyan bukata.

(4)Ko asamo Ziitir atafsa arika tauna shi Insha yana maganin wannan matsalar.

Kokuma atafasa shi sai adinga kuskura shi Insha yana maganin matsalar nauyin harshe, dakuma samun wahala wajan furta magana (inina).

(5)Ko asamo zuma mai kya sai ahada gishiri kadan arika gugawa akan harshe dakuma cikin bakin.
Wallahu aalam.

Rahamaniyya Islamic medicine Funtua.
Zaku iya bibiyarmu akan shafikanmu kamar haka :
magunguna.blogspot.com

Twitter @likitanci
Facebook :magungunan muslunchi.
Instagram username :likitanci Amuslunci.
  Ko ta email address 📧 markazusalaf@yahoo.com

Dafatan Allah yasa mudace Ameen.

No comments: