Wednesday, 2 November 2016

FASSARAR MAFALKI DAGA CIKIN LITTAFIN (FASSARAR MAFALKI NA IBINI #SEAREN.

Shahararan masani, kuma wanda Allah madaukakin sarki ya hore masa sanin fassarar mafalki, wato ibini serean.
Nasabar sa itace :Abunbakar  Muhammad ibini serin albasari.

Bayanin fassarar mafalki na Annabawa baki daya, da fassarar maanonin su, dakuma fassara mafalkin maaiki (SAW) akebe!!!
"""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""

Yace:Naji Abunbakar Ahmad dan Hussaini, dan Mahron Almakari yace:Nasiyo wata baiwa a tsammanina dai baturkace, maana yar kasar turkey ce, yace bata San harshenaba, kuma nima ban iya harshantaba, to a makobtansa akwai wasu bayin mata anan sai yazama na sai dai idan yayi magana sukuma sai su fassara mata.

Wata rana daga cikin rana ku wannan baiwa tasa ta kwanta tana barci kawai saada zata falka sai tafalka cikin kuka da kuma ehu, tana cewa ya shugabana dan Allah kasanar dani suratul fatihatil kitab.

Sai yace acikin ransa aa duba kaga jairar!!!
Wato dama taiya magana da harshena amma bata yiman magana dashi!

Yace daganan sai naje nakira wadannan bayin na makobtana amma bakin harshansa ba, amma lokaci daya kinyi masa magana dashi!!!

Daganan wannan baiwar sai tace wallahi nayi wani mafalki acikin barcina naga wani mutum mai tsananin kya acikin fushi mai tsanani, kuma ga wasu jamaa masu yawa suna biye dashi yana tafiya, sai natambaya nace wanene wancan?
Sai akace man Musa ne. Annabi Musa (AS).

Sai kuma ta hango wani kuma can shi kuma yafi wannan kya, maana yafi Annabi Musa (AS) kya sosai kuma atare dashi akwai jamaa masu yawa sunfi na Annabi Musa (AS) yawa kuma yanatafe suna biye dashi.

Daganan sai tasake tambaya cewa wanene kuma wancan?
Sai suka ce mata Annabi Muhammad (SAW) ne lallai bashakka wannan zanbi nima intafi tare da shi, daganan sai yaje wajan wata kofa ya kwankwasa ta sai aka bude masa kawai sai ya shige shida wadannan jamaan dasuke biye dashi.
Ikon Allah Ashe wannan kofa Aljanna ce.
Sai yarage saura wannan baiwar, dakuma wasu mata guda biyu, tace muma sai muka kwankwasa wannan kofar sai aka bude mana, wanda yabude masu wannan kofar sai Yace masu wanene acikin ku yake iya karanta suratul fatihatil kitab, dai dai?

Maana babu wanda zaa barshi yawuce sai wanda yaiya karanta suratul fatihatil kitab dai dai sannan ayi masa izni ya shige.

Wadannan matan kwara biyu dasuke tare daita sai suka karanta kawai suna gamawa aka basu izni akace suwuce.

Sai yarage saura Ita kadai kuma gashi takasa karantawa.

Daganan takara cewa ya aiki dan Allah kakoya man suratul fatihatil kitab, sai yaci gaba da koya mata cikin kunci dakuma wahala da kyar take rikewa, daganan har ta haddaceta daga ranar data hadda ce suratul fatiha kawai sai Allah yaamshi rayuwarta.

Sai sheikh Abu -said yace lallai mafalkin Annabawa amincin Allah ya tabbata agare su yace yana kasance wa daya ne daga cikin abubuwa guda kodai yazama bushara, Kokuma yazama gargadi gawanda yayi shi......... Wallahu aalam.

YA ALLAH KATADAMU TARE DA MANZON ALLAH SAW. ALLAHUMMA AMEEN.

Insha Allah zai cigaba da zuwa maku daga shafin mu na blogger :
Magunguna.blogspot.om

Ni nakaranta na kuma fassarar maku shi daga cikin littafin (Fassarar mafalki) na IBINI SEREAN.

No comments: