SHAJRATU MARYAM / ﺷﺠﺮﺓ ﻣﺮﻳﻢ/ ﻛﻒ ﻣﺮﻳﻢ
Shajratu Maryam wata itaciya ta flower mai yado
mai fitowa cikin ta siffar flowers kanana wadda tafi
yawa akasashe irinsu S/arabia,arewacin africa
(north Africa), iran dakuma Pakistan.
ita Shajratu tana fitowa ne da ganyaye,'ya'ya
dakuma karan icce(woody parts) wadda tafi yado
alokacin February zuwa April na kowace shekara.
Kasashen duniya da dama irinsu Malaysia suna
amfanida ita tunsama da shekaru daruruwa.
akashen dadama hakan sunanta yake misali ana
kiranta shajratu maryam,keff maryam,hand fatima
r.a(wato lallen fatima/shukar fatima r.a(yar
manzon Allah Saw) kamar yadda kuma ake
jinginata da sunan Maryam mahaifiyar Annabi Isah
A.s kuma har a bible akwai sunan wannan itaciya.
MAGUNGUNANDA TAKEYI.
shajratu maryam tana magunguna da dama gasu
kamar haka:
Kara karfin gabobi,maganin sanyi,wanke ciki,fito
da
fitsari cikin sauki,ciwon ido,lafiyar mai
jego,daidaita
jinin haihuwa,ciwon mara,karfin namiji(wurin
jima'i),fitar da aljani,maganin kuraje da
ciwuka,yoyon fitsari,fitarda sihiri na cikin ciki,kara
kuzari,rashin cin abinci,ciwon gabbai dss.
Likitocin zamani da sunyi bincike kan shajratu
maryam sun gano tana dauke da sinadaran
calcium, magnesium, potassium, zinc,iron. kuma
duk inda aka samu iccenda ke hade da sinadarin
calcium da magnesium to suna gyara gabbai sosai
da lafiyar jiki,sai gashi shajratu maryam ta hadasu.
Ana hada Garin shajratu maryam da man zaitun da
zuma arika don magance cututtuka da dama da
muka ambata asama,dakuma kariya daga
cututtuka. ana matsa ruwan ganyen shajratu
maryam ga mai ciwon ido da lafiyar idon koyin
farinsa.
Ana jikata ma asha ruwan donyi maganin sihiri da
ciwon gabbai,ana hadata da h/sauda da zuma
asha don korar shedanun aljannu da magance
sihiri. ana hadata da man zaitun ashafa ga ciwo
ko targade ko karaya. ana dafata da kanumfari
azuba asha kamar shayi don karin karfin da namiji
da kara masa ni'ima hakama dafa ita kadai asha
shima yana kara karfin namiji dakuma maganin
sanyi. hakama shanta na fito da fitsari cikin sauki.
ga wanda baya cin abinci zai iya zuba garinta cikin
abinci ko yasha da zuma.
Allah yasa adace.amin
Rahamaniyya Islamic medicine Funtua.
Email :markazusalaf@yahoo.com
Whatsapp no. 08062264060/08152753609
No comments:
Post a Comment