Showing posts with label Tambaya akan matsalar zafin fitsari. Show all posts
Showing posts with label Tambaya akan matsalar zafin fitsari. Show all posts

Thursday, 24 November 2016

Assalamu alaikum . Malam Allah Yakarama Basira,bayan Haka Mall.Wato Yau Kwana Uku Kenan Ina Fama Da Matsalar Fitsari Ina Jin Zafi Sosai Kafin Inyi Da Kuma Lkcin Da Yazo Karshe Kuma Wlh Mal.Gaba Daya Fitsarin Jini Ne Kuma Dana Gama Sai Inji Kamar Akwai Saura Amma Bazai Fito Duka Ba Sai Zuwa Anjima Kuma Ina Wahala Mal,dan Allah Malam AtaiMaka Kuma Wane Irin Ciwo Ne Wannan Mal.Kuma Ataimaka Min Da Maganin Gaggawa Dan Allah. Waalaikumu salam Dafarko inayi maka adduan Allah iyaye ma wannan matsalar Ameen. Wannan matsala kamar yadda masana sukayi bayani akai shine wannan matsalar bata rasa alaka da ciwon sanyi, wani lokaci kuma wasu sukace idan yazama kodar mutum batayin aiki yadda yakamata to bashakka mutum zai iya fuskantar wannan matsalar Wallahu aalam. Hanyar neman waraka daga wannan matsalar cikin sauri zaka iya hada Khal tuffa, da man zaitun da kuma zuma idan mutum yanada ciwon ulser sai yahada da ruwa kadan ya gauraya yasha insha Allah wannan zaa iya samun sauki da gaugawa. Sai kuma zaka iya hada garin habbatisauda dana yansun dakuma hulba, da kusdul hind karika tafasawa kanasha da zuma insha Allah zaka iya samun waraka daga wannan matsalar. Kokuma kasamo man habbatisauda karika zuba marfi daya aruwan shayi kana sha da madara. Kuma kana sha man habbatisauda tun daga kasan cibiyarka har zuwa kasan alauranka, safe da yamma wannan bayanin haka mai littafin (muujizati shifaa) yakawo acikin littafin # ALLAH yasaka masa da alkairi Ameen. Dafatan Allah yasa adace Ameen. Domin bincike a Shafinmu na blogger addaiwashifaa.blogspot.com