Sunday, 6 November 2016

Suriki mai hakuri, dakuma dattaku!!!

Hakika Allah madaukakin sarki yana cewa :Hakika zamucika maaunin maaunin masu hakuri da ladaddaki wadanda basuda iyaka. (suratul zumar)
انما يوفي الصبرون اجرهم بغير حساب.
Labari mai cike da mamaki :
Kamar yadda kuka sani halin yau da gobe ne yasanya wata baiwar Allah tayi yaji tatafi gidansu tabar gidan auranta!!!

Bayan tafiyarta saida ta kwashe tsawon wata shidda mijin nata baije ba kuma baitura biko ba!

Ana nan wata rana mahaifinta yafito   sai sukayi Karo da mijin nata, suka gaisa baiyi wata wataba sai yace haba malam wane yanzu ace iyalinka tatafi gidansu har wata shidda amma bakajeba kuma babu wanda ka aika!!!

Dabude bakin malam kawai sai yace  ai nadauka diyyar mutanan kirki nake aure......ooo

Wannan sirikin nasa bawan Allah dayake mutumin kirki baice masa Kala ba.

Da.. Zaije kasuwa yafito daga sai yafasa zuwa kasuwan yadawo gida Yace ma wannan diyyar tasa shirya kikoma gidan mijinki.
Tashirya takau koma abisa wannan ummarnin na mahaifinta.

Saikuma malam yafita yana zaune a majalissar sa inda yake zama..... Sai ga yara aguje baba kazo ma mammu tadawo yace kai madallah, to Kutsaya nazo... Malam yaje yayo cefane yabaiwa yayansa gashi kukai mata.

Sukaje suka kai mata daga nan
Ita kuma tayi abinci, daganan malam baikoma gidaba sai da dare yafara....... Yana shiga gida, uwar gida tace malam barka da dawowa, kadawao Lafiya ya ce lafiya kalau.

Sai aka kawo ma malam abinci, yana cikin cin abinci sai uwar gida tagaida shi, sai kuma tace haba malam yanzu ace naje gidanmu har tsawon wata shidda amma bakajeba!!

Sai uwar gida takara da cewa kuma gashi babana ma cewa yayi har zaginsa kayi!!!

Yace, eh, ke rabi dashi karya yake mutumin banza...!!!

Yanzu idan kaine sirikin wannan bawan Allah yazakayi?
Yake yar uwa idan kece matar wannan bawan Allah yazakiyi?

Hakika Allah madaukakin sarki ya ce"kyakyawan abu bazai tabayin dai dai da wanda yake mummuna ba, don haka kamar da kyakyawan abu gawanda ya munana maka.
Kuma wanda yazamo tsananin dashi akwai giyayya to kamayar dashi kamar dan uwanka shakiki, kuma wanda yake kaunar ka.
Amma babu wanda zai iya yin sai bayin Allah masu hakuri, sai kuma masu babban rabo. ((suratul fussilat))

Ya Allah kasanya mu daga cikin bayin ka masu hakuri, Dakuma Juriya, da yafiya gawadanda suka munana mana Ameen.

No comments: